Gwamnan Jihar Oyo, Ajimobi Ya Karya Campi.

Shugabannin jam'iyyar APC

Tun shekarar 1983 ba'a sake zaban wani gwamnan jihar Oyo ba domin ya yi wa'adi na biyu sai wannan karon

Gwamnan jihar Oyo Isiaka Abiola Ajimobi na jam'iyyar APC ya samu zarcewa wa'adin mulki na biyu abun da bai faru a jihar ba tun shekarar 1983. Gwamnan ya zama na faro da zai samu wa'adin mulki na biyu a jihar.

Wadanda gwamna Ajimobi ya kayar a zaben sun hada da tsohon gwamnan jihar Rashid Ladoja. Nasarar ta Ajimobi ta karya campin nan da ake yi a jihar cewa ba'a zabar gwamna mai ci karo na biyu.

To saidai jam'iyyar Accord Party taki ta sanya hannu a sakamakon zaben kamar yadda wakilinta Nureni Oladipo Adisa ya bayyana saboda zargin wai an yi magudi. Jam'iyyar ta hakikance sakamakon da aka bayar ba shi ne abun da ya wakana ba. Suna zargin an yi mirsisi.

Shi ko sakataren jam'iyyar APC reshen jihar Oyo Majid Olaiya godewa Allah ya yi saboda nasarar da suka samu. A wani hannun kuma tsohon gwamna Alao Akala wanda shi ma ya tsaya zaben shi da jam'iyyarsa sun yiwa gwamna Ajimobi muba'aya.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar Oyo, Ajimobi Ya Karya Campi - 2' 42"