Harakar tsaro ta tabarbare a Misira sumamman a haniyar Afirka. An samu matsalar tsaro a Mali, Libya da kuma arewacin Najeriya.
Abun dake faruwa matsala ce ta duniya gaba daya. Amma matsalar tabarbrewar tsaro a Najeriya nada nasabobi da dama. Na farko akwai maganar talauci kodayake talauci ba lallai shi ne dalili ba domin akwai wasu kasashen da suka fi Najariya talauci amma basu da rikici ko rashin zaman lafiya kamar Najeriya.
Akwai rashin fahimta na harkokin zamantakewa. Akwai kuma maganar 'yan ta'ada wadanda ba lallai ba ne 'yan Najeriya ne. Akwai masu anfani da kwaya, wato shaye-shaye da matasa keyi wanda ke jefasu cikin wani yanayi su yi abun da basu san suna yi ba.
Rashin isassun kayan aiki ga jami'an tsaro shi ma matsala ce da ta shafi tsaro. Akwai bukatar a mayar da hankali akan kayan aiki da horaswa.
Akwai bukatar a nemi tallafi daga kasashen waje kamar yadda Najeriya ta kira a yi mata amma yakamata a karfafa samun taimakon horaswa da kayan aiki ga jami'an tsaro. Idan an yi hakan to a nemi hadin kan duk masu ruwa da tsaki kamar sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma da na siyasa da na addini da dai sauransu. Idan an hada kai tsaro zai inganta.
Ya zama wajibi a tashi tsaye kwarai da gaske a Najeriya akan maganar tsaro.
A jihar Katsina ana samun zaman lafiya daidai gwargwado domin mutane basu rasa abun yi ba. Ya kamata a koma ga noma da kiwo domin su ne sana'o'i da aka gada.
Jami'an tsaro basu gaza ba sai dai shi jami'in tsaro akwai abun da za'a shimfida masa domin a taimaka masa da aikinsa. Yakamata a wayar da kawunan 'yan kasa akan yadda zasu sanarda jami'an tsaro idan sun ga abun da basu yadda dashi ba. Idan wani abu ya faru a shiadawa hukuma. Gwamnatocin jihohi kuma su ba jami'an tsaro tallafi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5