An samu rarrabuwar kawuna a majalisar dokokin jihar Bauchi, dangane da wasu kudurori da gwamnan jihar mai barin gado Muhammed Abdullahi Abubakar, ya bukaci majalisar dasu amince dasu, da suka hada da kirkiro da sabbin masarautu, da kuma soke wata kotu ta musamman da zata binciki gwamnan idan ya kammala wa’adinsa.
'Yan majalisu guda 17 cikin 'yan majalisu guda 30 sunki amincewa a dalilin rashin bin kaidar ayyukan majalisar ba.
Kamar yadda bincike ya nuna dokokin sun hada da na kirkiro da sababbin masarautu, da dokar da take soke izinin da gwamna yake dashi, don binciken gwamna a karshen wa’adin mulkinsa.
Sai kuma dokar da 'yan majalisar keson aiwatarwa don a rika biyansu kudaden fansho na wata wata a karshen zamansu a majalisa, koda shike ba a gabatar da wannan batunba a kwaryar majalisar.
Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar, Abdullahi Abdulkadir shine ya karanta kudurorin da gwamnan ya aiko dasu domin su amince da su.
Sai dai a bangaren masu adawa da kudurorin sunce sam ba abi doka ba, kamar yadda dan majalisa dake wakiltar mazabar Lere Bula Muhammad Aminu Tukur yayi bayani a tattaunawa dashi ta wayar tarho.
A cewar wani mai sharhi akan siyasa Kwamred Abdullahi Koli, wannan abu neman hada rikicine tsakanin gwamnati mai ficewa da kuma mai shigowa.
Har ila yau naji ta bakin wani mai sarautar gargajiya dangane da samar da wannan kudurin.
Ga cikakken rahoton: Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5