Gwamnan Jihar Adamawa Ya Sallami Ma'aikata Fiye Da 300

Ma'aikata A Najeriya

Tun farkon hawansa a watan Mayun wannan shekarar gwamnan jihar Adamawa dan jam'iyar PDP, Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana aniyarsa ta soke daukan ma'aikatan da tsohuwar gwamnatin APC ta Senata Muhammadu Umaru Jibrilla Bindow.

Tuni har an baiwa wasu ma'aikatan kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar takardar sallama, dalilin da ya sa wadanda abun ya shafa kiran taron manema labarai.

Wani ma'aikaci cikin su, Faisal Baba na cikin wadanda suka yi jawabi ga manema labaran, ya kuma bayyana halin da suke ciki.

Wakilin Muryar Amurka ya tambayi wasu daga cikinsu ko yaya jam'iyar APC wanda gwamnatin ta ne ta dauki wadannan ma'aikatan ke cewa Ahmad Lawal sakataren tsare tsare na jam'iyar, ya kara haske game da lamari.

To sai dai kuma gwamnan jihar Adamawan ta bakin Daraktan yada labaransa Solomon Kumangar ya ce da kyakkyawar manufa a korar ma'aikatan.

Ga rahoto a sauti daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar Adamawa Ya Sallami Ma'aikata Fiye Da 300