Rundunar tace ta hana 'yan bindigan shiga Maiduguri da Kondiga da kuma kwace makamai da dama.
Babban jami'in sojojin Najeriya mai kula da hulda da jama'a Janaral Kolade a wani sako da ya aikawa manema labarai yace rundunar ta samu nasarar fatattakan maharan a Maiduguri da garin Konduga har sau biyu. Yace sun takawa maharan birki yayin da suke kokarin ganin yadda zasu kwato garin Mongunu da yanzu yake hannun maharan.
Yace sojojin sun janye ne bayan raunin da aka jima kwamandansu dake kula da shiyar garin Mongunun. Yace sun kashe maharan da dama sakamakon arangamar da suka yi dasu jiya kuma suna gudanar da bincike domin su zakulo sauran maharan.
Tuni dai aka samu kwanciyar hankali a birnin Maiduguri inda harkokin yau da kullum na cigaba. Gwmnan jihar Borno Kashim Shettima ya jajantawa al'ummar jihar sumamman wadanda suka rasa 'yanuwa a Maiduguri da Kondiga. Yace suna nan tare da jama'a ko su yaru ko su mutu ba zasu bar jama'a ba. Ya kara da kiran mutane su shaidawa jami'an tsaro duk abun da suka gani basu yadda dashi ba.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5