Gwamna Kabir Ya Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Masarautun Kano

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu akan sabuwar dokar da majalisar dokokin jihar ta yi wa kwaskwarima da ya rushe masarautu biyar a jihar. Da safiyar yau Alhamis ne Majalisar ta yi wa dokar masarautun Kano ta shekarar 2019 garambawul, inda ta soke duka masarautun jihar biyar.