Kamar yadda wakiliyar Muryar Amurka a Abuja Halima Abdulrauf ta ruwaito, iyayen daliban na jami’ar gwamnatin tarayya dake Gusau wanda 'yayansu ke hannun ‘yan bindigar tun bayan da suka sace su a ranar 22 ga watan satumban 2023 da ta shude, sun sake mika kokon barar su ga gwamnatin jihar Zamfara da na tarayyar Najeriya da su dube su da idanun Rahama.
Wata kungiyar da ake ayyana ta da Voice of Arewa ce ta yi gaba, a madadin iyayen yaran da aka sace, a yau litinin.
A zantawarsa da Muryar Amurka, daya daga cikin iyayen daliban da ke hannun 'yan bindigar, Hafiz Jamo, yace lallai ba kudi ne ‘yan ta’addan suke nema a wajen su ba.
Ya ce abin da suke so shi ne a yi musayar ‘ya’yansu da mutanensu dake tsare a hannun hukumomin tsaro.
A wani bangaren kuma, Sakataren Yada Labarai na kungiyar ta Muryar Arewa wato Voice of Arewa, Muhammad Salis, wanda ya kasance daya daga cikin kungiyoyi masu fafutukar ganin an sako daliban jami’ar tarayyar na Gusau, yace mataki na gaba da zasu dauka, shi ne ganawa da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, domin su sake kai kokensu don ganin an sako daliban.
Da wakiliyar tamu ta tuntubi gwamnatin jihar Zamfara don jin ra'ayin su a game da wannan bukatar ta iyayen dalibai matan da aka sace, Gwamnan Jihar, Dauda Lawal, yace gwamnatinsa tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya na yin duk mai yiyuwa wajen ganin an kubutar da daliban kuma da yardan Allah, gwamnati zata ceto su.
Tun bayan sace daliban daga jami’ar, matsalar sace-sacen don neman kudin fansa ya kara kamari.
Na baya bayan nan da ya faru shi ne sace mutane 7 ‘yan gida daya a birnin tarayya Abuja, wanda ya hada da magidanci da yaransa 6, kamar yadda Adamu Asiya, 'yar uwa ga wadanda aka sace ta bayyana.
Ta ce 'yan bindigar sun sako mahaifin yara shidan daga baya domin ya samo kudin fansar da suka bukata, naira miliyan 60, wato ko wanne daga cikin yara shidan, za a fanso shi da naira miliyan goma.
Satar mutane don neman kudin fansa ko kuma amfani da mutanen da aka sace a matsayin wani garkuwa don yin musayar fursunoni tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga, ya zama ruwan dare a yankin arewa maso yammacin Najeriya a ‘yan shekarun bayan nan, inda wasu gungun ‘yan bindiga ke kai hare-hare kan kauyuka, makarantu har ma da matafiya, inda suke neman kudin fansa na miliyoyin naira sannan a wani bangaren kuma suke hana mutane yin balaguro ko noma sakamakon tare hanya da suke yi.
Masana tsaro dai na kara jadadawa gwamnatoci dukkanin matakai masu mahimmancin fitar da dabarun kula da gandun daji inda suka zama tamkar maboya ga gungun mutanen.
A saurari rahoton Halima Abdulrauf
Your browser doesn’t support HTML5
: