Gwaje-gwajen Riga Kafin COVID-19 Na Da Muhimmanci - Dr Fauci

An dakatar da gwaje-gwajen maganin riga kafin COVID-19 na kamfanin AstraZeneca, abinda Dr. Fauci ya ce hakan ya nuna cewa ana kokarin tabbatar da ingancin magungunan.

Yayin da adadin wadanda suka mutu sanadiyyar annobar coronavirus a fadin duniya ya zarta mutum 900,000, kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa na Amurka ya ce, dakatar da gwajin riga kafin kamfanin AstraZeneca a matakin karshe, kamfanin da ke daga cikin masu hada magungunan COVID-19 da ake gwadawa a fadin duniya na nuna cewa da gaske ake wajen tabbatar da ingancin magungunan a gwaje-gwajen da ake yi.

A wata hira da gidan talabijin din CBS, Dr. Anthony Fauci, shugaban cibiyar kula da cututtuka ta kasa, ya ce "ya na da matukar muhamanci a lura cewa gwaje-gwajen da ake yi a matakai dabam-daban, ana yi ne don tabbatar da cewa lallai maganin bai da wata illa ga bil'adama.

Babban kanfanin mallakar kasashen Burtaniya da Sweden, ya dakatar da gwajin ne bayan da wani daga cikin mutanen da suka amince a yi gwajin kansu ya fara rashin lafiya bayan ya sha maganin.

"Wannan babban abun takaici ne, amma muna fatan zasu iya ci gaba da sauran gwaje-gwajen maganin, a cewar Fauci. Amma bamu sani ba. Akwai bukatar a zurfafa bincike.

Kamfanin dai ya fitar da sanarwa a ranar Talata ya na cewa dakatar da gwajin maganin wani mataki ne da dama ake bi, dole ne a bi shi idan aka samu rasihn lafiyar da ba a san yadda ta fara ba a matakan gwaje-gwajen, yayin da ake bincike kan maganin, don tabbatar da ingancin gwaje-gwajen.