Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, kan mummunar arangamar da ta auku akan iyakar Isra’ila da yankin Gaza a jiya Juma’a.
Arangamar ta yi sanadin mutuwar Falasdinawa 15, kana wasu 1,400 suka jikkata, ciki har da mutane 750 da suka ji raunuka sanadiyar harbin bindiga.
A jiya Juma’a kwamitin Sulhu na Majalisar ya gudanar da wani taron gaggawa, domin tattauna takaddamar da ta kaure a yankin na Gaza.
Amma ba a cimma wata matsaya ba.
Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya, Danny Danon, ya ce an gudanar da taron gaggawan, duk da cewa Amurka da Isra’ila sun kalaubalanci hakan, inda suka yi kira da a dage zaman har sai an kammala wani bikin Yaduwa da suke yi a daidai wannan lokaci.
Rikici ya barke ne a lokacin da dubban Falasinawa suka nufi kan iyakokin yankunan biyu, lamarin da dakarun Isra’ila suka ce sun maida martani akan masu jifan su da duwatsu.
Ma’aikatar kiwon lafiya a Falasdinu ta ce dakarun Isra’ila sun yi amfani da harsashi na asali da yaji mai sa kwalla wajen tarwatsa mutane.
Wannan arangama ita ce mafi muni da ta auku a yankin na Gaza da ke cikin yankin Falasadinu, tun bayan yakin 2014 da aka yi tsakanin Isra’ila da Hamas.