Kungiyar ‘yan tawaye mafi girma dake lardin Ghouta na kasar Syria yace ya cimma matsaya da sojojin Rasha domin a kwashe wadanda aka jima rauni kana kuma su bar masu aikin jin kai sui kai ga isa a wuraren da ‘yan tawayen suke rike dashi a gabashin Ghouta.
Kungiyar ta ‘yan tawaye, Failaq al Rahman ya fada a cikn wata sanarwa jiya jumaa cewa fararen hular da suka amince suci gabada zama a yankin gabashin na Ghouta ana basu tabbacin cewa za a kare su.
Yanzu haka dai ana sa ran ‘yan sandan kasar Rasha su kasance a wuraren dake karkashin kulawar kungiyar ta Failaq al-Rahman ciki ko harda gefen garin Arbeen,Zamalka, Ein Tarma da Jobar.
Haka kuma kungiyoyin biyu sun amince da musayar hursunoni har su dubu 3 da dari biyar da kungiyar ‘yan tawaye ke rike dasu.
Hai ila yau kafar yada labarai na sojan kasar ta Syria ya bayyana cewa akwai wata yarjejeniya da aka cimmawa tsakanin gwamnatin kasar ta Syria da masu dauke da makamai dake unguwannin garin na Ghouta da suka hada da Arbeen,Zamalka,Hazeh da Joba, ‘Yan tawayen zasu kwashe yanasu-yanasu su dunfari Arewa maso yammacin gundumar Idlib.
Kanfanin dillacin labarai nakasar ta Syria SANA, yace sama da mutane dubu 4 ne suka bar Ghouta a jiya jumaa kana wasu da suka kai dubu 6 sun wuce ne tun kafin ma jiya jumaan.
Shugabannin ‘yan tawayen sunce suna sa ran wannan kwashewar ya dan dauki kwanaki mai tsawo ana yin sa.
Duk wadannan yarjejeniyoyin dai kasar Rasha ceta tsara shi tsakanin ‘yan tawayen da gwamnatin kasar ta Syria, ciki ko harda musayar hursunoni, wannan yasa iyalan mayakan suka bar wurin ciki kwanciyar hankali.
Facebook Forum