WASHINGTON DC - A ranar 28 ga watan Fabrairun daya gabata, hukumomin Najeriya suka tsare Shugaban Sashen Yaki da laifuffukan Kudi da Kiyaye Doka na Binance, Tigran Gambaryan da Manajan Kamfanin me Kula da Shiyar Afrika, Nadeem Anjarwalla.
Duk da cewar Anjarwalla ya tsere daga hannun hukumomin tsaron Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro, ana sa ran gwamnatin tarayyar Najeriya ta tuhumi kamfanin da dukkanin shugabanninsa 2 akan laifuffukan kin biyan haraji da halasta kudaden haram.
A ranar 25 ga watan Maris din daya gabata, Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Tarayyar Najeriya (FIRS) ta tuhumi kamfanin Binance Da Laifin Kin Biyan Haraji.
A cewar FIRS, manufar shigar da tuhumar shine tabbatar da alkinta kudade da kiyaye martabar tattalin arzikin Najeriya.
Rahotanni na cewar, karar da firs ta shigar na tuhumar Binance da zarge-zargen kaucewa biyan haraji.
A yayin fara sauraran karar, lauyan bangaren masu kara, Moses Ideho, yace sun gaza mika sammaci ga Gambaryan saboda sun kasa samunsa.
A Cewar Ideho, "ya me girma mai shari'a, bangaren masu kara ya gaza mika sammaci ga wanda ake kara na 2 (Gambaryan). Saboda hakan muka nemi masinjan kotu ya mika shi ga wanda ake kara na 1, inda nan ma aka hana shi kaiwa gare shi.
Daga bisani, Ideho ya bukaci kotun ta sahale masa mika sammacin ga wanda ake karar a gabanta.
Bayan mika sammacin ga wanda ake karar, bangaren masu karar ya bukaci kotun ta dan jinkirta ko kuma ta dage sauraran karar zuwa wani lokaci anan gaba domin baiwa wanda ake tuhumar damar ganawa da lauyoyinsa.
Kasancewar ba'a samu wani kalubale daga lauyan wadanda ake kara, Emeka Nwite ba, yasa alkalin kotun dage sauraran karar zuwa ranar 19 ga watan Afrilun da muke ciki domin gurfanar da wadanda ake tuhuma.
Babu dai lauyan daya wakilci kamfanin Binance da Anjarwalla a zaman kotun.