Gugugwar da aka lakabawa sunan Nate, ta kara karfi a yau Asabar yayinda take ratsawa ta tsakiya gabar Mexico, a dai dai lokacinda ta doshi gabar ruwan Amurka, inda ake sa ran zata dira a doron kasa a daren yau Asabar agogon Amurka, kamar yadda cibiyar kula da yanyi ta Amurka tayi bayani.
Tuni guguwar ta kara karfi inda take kadawar kilomita 150 cikin ko wani sa'a daya, ana jin Nate zata kara karfi zuwa rukuni na biyu kamin ta ta iso doron kasa ta gabar arewacin Amurka.
Tuni aka kada gurji gargadi na aukuwar guguwa dauke da ruwan sama kama daga Lousiana zuwa kan iyakokin Alabama da Florida.
Manya-manyan tashoshin jiragen ruwa dake fadin tsakiyar gabar Amurka sun rufe a yau Asabar, yayinda guguwar take kara karfi, har ake jin ruwan tekun zai haura zuwa kafa tara.
Shugaban Amurka Donakd Trump ya ayyana dokar ta baci mataki da zai bada damar a bada agajin gaggawa ga yankunan da abun ya shafa saboda rage radadin guguwar.