Shugaban Amurka Donald Trump yana shirin kai ziyara jihar North Carolina yau Laraba, domin ganewa idonsa irin barnar da guguwar da aka ba lakabi da Florence tayi, da kuma aikin tallafawa wadanda lamarin ya shafa da ake gudanarwa.
Trump ya rubuta a shafinsa na twitter jiya talata cewa, “Kowa yana cewa muna kokari dangane da guguwar Florence- kuma gaskiya suka fada dari bisa dari.”
Ya bayyana jami’an agajin gaggawa da sojoji da kuma wadanda suke fara kai agaji idan bala’I ya auku a matsayin jarumai’ sai dai Trump ya kushewa ‘yan jam’iyar Democrat da cewa, nan ba da dadewa ba zasu fara karya cewa, matakan da aka dauka bayan aukuwar guguwar shirme ne.”
Shugaban kasar ya fusata yana gani cewa, Karin gishiri ‘yan jam’iyar Democrat suka yi kan adadin wadanda suka mutu a guguwar da ta auku bara a Puerto Rico domin bata mashi suna.