Guguwar "Florence" Ta Haddasa Asarar Rayuka a Amurka

Ma'aikatan ceto sun kubutar da wani mutu

“Za a ci gaba da ganin tumbatsar ruwa a gabar tekun Carolina a yinin Asabar, a wasu yankuna ma har zuwa daren Lahadi da wayewar garin Litinin.” Inji Chris Wamsley, jami’i ne a hukumar da ke nazarin yanayi a Amurka.

Kusan gidaje da wuraren kasuwanci miliyan daya ne ke zaune babu wutar lantarki, yayin da mummunar guguwar Florence take ci gaba da abkawa wani yankin kudancin Amurka.

A yau Asabar cibiyar da ke sa ido kan aukuwar guguwa ta Amurka, ta ce wannan bala’i na ci gaba da haifar da ambaliyar ruwa a jihohin Carolina ta Arewa da ta Kudu.

Cibiyar ta kara da cewa akwai yiwuwar a kara fuskantar matsananciyar gugugwa a yau Asabar a kudu maso gabashin jihar Carolina ta Arewa da kuma arewa maso gabashin jihar Carolina ta Kudu.​

“Za a ci gaba da ganin tumbatsar ruwa a gabar tekun Carolina a yinin Asabar, a wasu yankuna ma har zuwa daren Lahadi da wayewar garin Litinin.” Inji Chris Wamsley, jami’i ne a hukumar da ke nazarin yanayi a Amurka.

‘Yan sanda a yankin Wilmington sun ce wata mata da jaririnta sun rasa rayukansu, bayan da bishiya ta fado akan gidansu.

Sannan wata mata daban ta rasu sanadiyar matsalar bugun zuciya, bayan da jami’an kiwon lafiya masu ba da agajin gaggawa suka gaza kai wa gareta, saboda bishiyoyi da suka fadi suka tattare hanyoyi.

Baya ga haka, wutar lantarki ta kashe wani dattijo mai shekaru 78, sannan ta halaka wani mutum daban, wanda ya iska ta yi wurgi da shi, a lokacin da ya fita neman karensa da ya bata.