Guatemala Da El Salvador Sun Tura Dakaru Zuwa Haiti

Haiti Gang Violence

Shugabar gwamnatin rikon kwarya ta Haiti, Leslie Voltaire, tare da Firayim Minista Alix Didier Fils-Aime da jakadan Amurka Dennis Hankins, sun yi maraba da sojojin a filin jirgin saman Port-au-Prince,

Wata tawagar jami'an tsaro daga Guatemala da El Salvador sun isa babban birnin kasar Haiti a jiya Juma'a, domin karfafawa aikin da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya da aka dade ana samun tsaikon sa, na maido da tsaro a rikicin da ya barke tsakanin kungiyoyin da ke dauke da makamai.

Sabbin dakarun sun hada da na kasar Guatemala 75, da 'yan Salvador 8, a cewar jami’in sadarwa na rundunar.

Shugabar gwamnatin rikon kwarya ta Haiti, Leslie Voltaire, tare da Firayim Minista Alix Didier Fils-Aime da jakadan Amurka Dennis Hankins, sun yi maraba da sojojin a filin jirgin saman Port-au-Prince, kamar yadda gwamnatin ta rikon kwarya ta Haiti ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumunta.

A cikin watan Nuwamba, shugaban kasar Guatemala, Bernardo Arevalo, ya yi alkawarin aika sojoji 150, watanni uku bayan alkawarin da ya yi a cikin wata wasika zuwa ga Majalisar Dinkin Duniya, na aikewa da dakaru da ba’a bayyana adadinsu ba, tare kuma da kayan aiki.

Ita kuwa El Salvador a cikin watan Agusta, ta yi alkawarin ba da sojoji 78 domin ayukan kwashe jama’a da kula da lafiya, tare kuma da jirage 3 masu saukar angulu da jami’an tsaron Haiti ke matukar bukata, domin aikin cikin tsaunuka da kwazazzabai, da kuma manyan hanyoyi da ke tattare da shingayen bincike na kungiyoyin ‘yan ta da kayar baya.