GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Yuni 14, 2018:Tsarin Ciyar Da Yara A Makarantun Gwamnatin Najeriya Kashi Na Biyu

Grace Alheri Abdu

Bayan shekaru biyu da kaddamar da shirin ciyar da kananan yara da abinci a makarantun gwamnati na Najeriya, da kawo yanzu ake gudanarwa a jihohi ishirin da hudu na kasar., bincike ya nuna shirin yana cike da kurakurai da matsaloli, kama daga rashin bada kudi akai akai ga masu dafa abincin zuwa yanayin rashin tsafta da inganci.

Yayin nazarin shirin, mun kuma tarar ana zubawa yara abinci akan takardar littafansu a wata makaranta a birnin Kano, bincikenmu ya kuma nuna, wabin da ake samu wajen aiwatar da shirin a jihar Kano na daga cikin kalubalen da shirin ke fuskanta.

Tuni dai masu bibiyar yadda wannan shirin ke tafiya ke bayyana fargaba kan irin wannan abinci da gwamnatin ke baiwa daliban. Dr Usman Muhammad Ibrahim na sashin kula da cutukan al’uma ya fayyace matakan tabbatar da tsaftar abinci musamman ga kananan yara dalibai. Yace ana fara tsabtace abinci ne tun daga gona inda ake noma shi,

Kamar yadda muka alkawarta muku makon jiya, mun nemi jin ta bakin hukumar CRC da aka dorawa alhakin sanya ido akan yadda shirin ciyar da daliban ke tafiya a jihar Kano. Ta kuma amince cewa akwai kalubalai da suka dabaibaye shirin, amma tace tana daukar matakai. Alhaji Sagiru Gambo ‘Yanmusa sakataren hukumar yace babbar kalubalar da ake fuskanta ita ce, daga cikin mata 13470 da aka tantance domin kwangilar dafa abincin, wadanda ke samun kudin aikin ba su kai rabin haka ba kuma su-ma ba sa samu akai-akai.
A cikin hirarsu da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari, ya bayyana rawar da hukumar CRC ke takawa a aiwatar da shirin.

Saurari shirin domin jin cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Tsarin ciyar da yara da abinci-Kashi na biyu:10:14"