Jiya rundunar ‘yan sandan Najeriya a Maiduguri ta bayyana cewa, mutane takwas da ta kama da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun amsa cewa, suna da hannu a sace ‘yammatan Chibok dari biyu da saba’in da shida a watan Aprilu shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, jiya din ne kuma har wayau, wata kungiyar kiristoci ta gudanar da gangami a kofar ofishin jakadancin Najeriya dake birnin London inda ta mika koke da bukatar dawo da Leah Sharibu, daliba daya tilo da kungiyar Boko Haram ta saki, sabili da taki Musulunta bayan saceta da wadansu dalibai mata a makarantar sakandare ta Dapchi kwanaki dari da hamsin da da suka shige, tana da shekaru goma sha biyar.
Banda haka kuma jiya Laraba ne kuma tsohuwar shugabar kasar Maurishos Prof Ameenah Gurib-Fakim ta gana da wadansu iyayen ‘yammatan na Chibok da kuma Dapchi da har yanzu ba a dawo da ‘ya’yansu ba, a Lagos, duk da yake ba a bayyana abinda ta tattauna da suba. To zamu ci gaba da bin diddigin wadannan batutuwan da kuma ci gaba ko akasin haka da ake samu.
A yau dai shirin ya yada zango ne a Jamhuriyar Nijar, inda, makon da ya gabata, mataimakiyar babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta jagoranci wata tawaga zuwa Jamhuriyar Nijar inda ta ganewa idonta matsalolin da mata ke fuskanta.
A jawabinta ga manema labarai, bayan ta zaga jihohin Maradi da Nyamai, Hajiya Amina Mohammed ta bayyana cewa, akwai bukatar karin tallafin Majalisar Dinkin Duniya domin taimakawa mata su yaki talauci.
Kafin ziyarar ta Hajiya Amina Mohammed, hukumomi a jamhuriyar Nijar sunyi wani gagarumin taro da ya hada kan masu ruwa da tsaki domin neman shawo kan matsalolin dake addabar mata.
Bayan taron ne kuma Shirin Domin Iyali ya zauna da wadansu maharta taron domin bada gudummuwa ga wannan yunkurin.
Your browser doesn’t support HTML5