Makon jiya muka fara nazari kan yanayin da aka shiga inda ake kara samun ma’aurata suna kuntatawa abokan zamansu da ya shiga kaiwa ga kisa, akasin abinda aka saba gani a lokutan baya. Ta haka shirin Domin Iyali ya gayyaci masana da majibantan wannan lamarin domin neman gano masababin lamarin da kuma matakan shawo kanshi.
WASHINGTONB, DC —
A yau ma muna tare da bakin namu, Barrister Maryam Ahmed wata lauya kuma ‘yar gwaggwarmayar kare hakin iyali, da Mallam Abba Bello, jami’in Kungiyar dake aikace aikacen kiwon lafiyar iyali, da kuma Dr, Haruna Yakubu na sashen kula da lafiyar kwakwalwa a asibitin koyarwa na Aminu Kano duka a birnin Kano.
Jagoran wannan tattaunawa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya tambayi Dr Haruna Yakubu ko wannan lamarin yana da nasaba da canfin da wadansu ke yi cewa shafar aljannu ne, ko tabun hankali, kasancewa lamarin ya shafi talakawa da attajirai, masu ilimi da kuma marasa ilimin Boko.
Saurari cikakken bayanin nasa da na sauran kwararru a shirin na yau.
Your browser doesn’t support HTML5