GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Mayu 10, 2018: Ranar Karrama Iyaye Mata

Grace Alheri Abdu

Ranar Lahadi sha uku ga watan Mayu, ake burkin ranar iyaye mata, ranar da ake karrama uwaye, da irin tasirin mata a al'umma musamman a tsakanin iyali.

An fara bukin wannan ranar ne a nan Amurka a shekara ta dubu da dari tara da takwas lokacin da wata 'yar gwaggwarmayar wanzar da zaman lafiya da tayi aikin agazawa sojojin da suka ji rauni daga dukan bangarorin da suka gwabza yakin basasa a Amurka, ta shirya addu'oin tunawa da mahaifiyarta yayin cika shekara guda da rasuwarta.

Bayan ta cimma nasarar samun goyon bayan kebe rana domin karrama iyaye mata, ake daukar ranar da muhimmanci a Amurka, har ta kasance daya daga cikin lokutan da Amurkawa suke kashe kudi ainun wajen sayen kyautai da gudanar da shirye shirye dabam dabam domin karrama iyaye mata.

To shirin Domin Iyali ma ba a barshi baya ba. Mun kuma dace mun sami tsohuwa da take da zuri'a hudu mata watau ita kakar, da 'yarta, da jikarta, da kuma tattaba kunnenta. Ga abinda suke cewa game da wannan rana.

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Karrama Iyaye Mata-9:55"