Kungiyar Boko Haram ta ci gaba da rike Leah Sharibu dalibar makarantar sakandaren Dapchi guda daya tilo da kungiyar ta koma da ita, sabili da taki Musulunta, bayan dawo da sauran ‘yammatan da suka rage da rai, da ta sace ranar goma sha tara ga watan Fabrairu, ta kuma dawo dasu ranar da suka cika kwanaki talatin a hannunta.
Wannan na faruwa ne ana saura kwanaki goma sha shida a cika shekaru hudu da sace 'yammatan sakandaren Chibok, da har yanzu, kungiyar ke rike da dari da goma sha biyu, da babu tabbacin inda suke, ko suna nan da rai duka, ko kuma halin da suke ciki.
Na zanta da mahaifin Leah, Nathan Sharibu wanda yace har I zuwa lokacin da muka yi hira dashi, babu wata hukuma da ta tuntubeshi dangane da batun ‘yarshi da aka ki saki. Ya fara da yadda yaji bayan samun labarin dawo da yammatan.
A cikin hirarmu da shi yayin ziyararsa a ofishinmu , Lauya mai zaman kansa Yakubu Saleh Bawa ya bayyana takaicin gaza kama mayakan ko dai lokacin da suka shiga garin Dapchi kamin sace ‘yammatan ko kuma bayan dawo dasu ido na ganin ido.
Saurari cikakken shirin.
Your browser doesn’t support HTML5