Wannan na faruwa ne ana saura mako uku a cika shekaru hudu da sace 'yammatan sakandaren Chibok, da har yanzu kungiyar ke rike da dari da goma sha biyu, da babu tabbacin inda suke, ko suna nan da rai duka, ko kuma halin da suke ciki.
Yayinda ake farincikin dawowar 'yammatan, yanayin sace su da yazo daya da yadda aka sace 'yanmatan Chibok, ya zama wani abu da ya haifar da kila wakala, banda haka kuma, tambayar dake zukatan da dama bayan dawo da yammatan Dapchi ita ce , menene ya hana jami'an tsaro kama mayakan bayan sun ajiye 'yammatan?.
Wakilinmu Haruna Dauda Bi'u yayi hira da shugaban kungiyar iyayen yammatan sakandaren Dapchi Bashiru Alhaji Manzo bayan ganawarsu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari makon da ya gabata.
Bayan samun labarin dawo da 'yammatan, Haruna ya kuma zanta da wani dan jarida da yake cikin ayarin wadanda suka fara isa wurinda aka sauke 'yammatan.
Saurari Cikakken shirin.
Your browser doesn’t support HTML5