GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Fabrairu, 2, 2018, Hira Da Hajiya Aisha Buhari Kan Cin Zarafin Iyali A Gida

Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari da Grace Alheri Abdu

A ci gaba da nazarin matakan shawo kan cin zarafin jama'a a cikin iyali kama daga ma'aurata da ’yayan da suka haifa, ko 'yan riko, ko kuma masu aiki a karkashinsu, yau shirin Domin Iyali ya karbi bakuncin uwargidan shugaban kasar Najeriya Hajiya Aisha Buhari wadda ganin munin lamarin ya sa ta hada kan kungiyoyi da masu ruwa da tsaki da nufin bada gudummuwa a yunkurin shawo kan lamarin. A cikin hirarsu da wakilinmu Hassan Maina Kaina, Hajiya Aisha Buhari tayi karin haske game da taron.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Hajiya Aisha Buhari-10:24"


Binciken da wata kungiyar mai zaman kanta da ake kira CLEEN a takaice ta gudanar na nuni da cewa, ana cin zarafin mutun daya cikin uku a cikin iyali, yayinda tashin hankali da gallazawa abokan zama yake karuwa. Nan gaba a shirin zaku ji tattaunawar da shirin ya yi da masu ruwa da tsaki da nufin neman hanyar shawo kan irin wannan matsala. A ganinku, Menene ke haifar da cin zarafin kananan yara ko abokan zama a cikin iyali kuma yaya za a iya magance matsalar? Sai ku ci gaba da kasancewa da shirin Domin Iyali.