Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Janairu 18, 2018, Cin Zarafin Yara A Gida: Kashi Na Daya


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Makon da ya gabata kungiyar Boko haram ta fitar da wani sabon faifan bidiyo inda aka nuna wadansu daga cikin ‘yammatan sakandaren Chibok da suka rage a hannun Kungiyar tareda gungun wasu matan da akace 'yansanda ne da suka shiga hannun mayakan.

Daga cikin 'yan matan da akace 'yan Chibok ne, an ga wassanye da hijabi wadansu kuma da nibaki, wadansu daga cikinsu kuma suna rike da kananan yara. Daya daga cikinsu wadda tayi jawabi da Hausa da kuma harshen Chibok tace ba zasu koma wurin iyayensu ba ta kuma godewa shugaban kungiyar da ta kira Baba Shekau da tace yana lura da su sosai. Tace suna jin dadin zabin da suka yi ta kuma yi kira ga iyayen su tuba.

Ta gefen matan 'yansanda kuma an nuna su suna kira ga gwamnatin tarayyar Nigeria ta zo ta cece su don su koma ga iyalinsu. Zamu yi nazarin lamarin wadannan ,atan duka nan gaba.

A yau, zamu maida hankali ne akan yadda kishi yake sa wadansu mata su ci zarafin ya’yan abokan zamansu abinda wadansu lokatai yakan kai ga karshen kwana. Kafin mu hada kan masu ruwa da tsaki domin neman hanyar shawo kan wannan matsala, bari muyi shinfida da irin wannan lamari da ya faru kwanan baya a jihar Kano. Ga Wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari.

Domin Iyali-10:26"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:26 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG