GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Agusta 09, 2018:Rahoto Na Musamman Kan Matsalar Shan Miyagun Kwayoyi

Grace Alheri Abdu

Manazarta sun dade suna cewa, matasa sune rukuni na samar da ci gaban kowacce al’umma, sai dai abinda yafi taba zukatan jama’a dangane da matasa a halin yanzu shine yadda suka rungumi shan miyagun kwayoyi barkatai, lamarin da ake gani yayi munin gaske da Kamari a yankin arewacin Najeriya

Wani babban al’amari mai tayar da hankali shine, yadda bincike ya nuna cewa, adadin mata masu shiga shaye shayen miyagun kwayoyi, yana kokarin zarce na maza, kama daga ‘yammata, da manyan mata, kai har ma da matan aure, lamarin dake barazana ga dorewa da ci gaban iyali.

Ta haka shirin Domin Iyali zai nazarci wannan batu domin fadakar da iyaye kan wannan matsala da kuma neman matakan shawo kan wannan lamari.

A cikin hirarsu da wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna, yayinda shirin ke gudanar da bincike kan wannan matsala, kwamandan hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta Najeriya a jihar Sokoto Musbahu Idris, ya zayyana abubuwan da matasa a arewacin Najeriya suke sha domin samun maye. Yayinsa kwararru a fannin kiwon lafiya da zamantakewar al'umma suka bayyana illar shan miyagun kwayoyi.

Saurari cikakken shirin

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoto na musamman kan shan miyagun kwayoyi a Najeriya-11:30"