Idan kuna biye damu Shirin Domin Iyali ya karbi bakuncin wadansu maharta taron karawa juna sani kan kare hakkokin mata a Jamhuriyar Nijar da ya hada kan masu ruwa da tsaki sa suka hada da kungiyoyin mata, sarakunan, gargajiya, shugabannin al'umma, 'yan jarida, magidanta da kuma 'yan gwaggwarmaya, da nufin shawo kan mace macen aure da kuma wadansu matsaloli da suke hana ci gaban Iyali.
Yau ma muna tare da Usman Dambaji shugaban kungiyar 'yan jarida da ake kira Rejiya, da kuma madam Kako Fatuma shugabar hadakar kungiyoyin mata da ake kira kwangafen. jagoran tattaunawar Yusuf Abdullahi ya tambayi Madam Kako ko basu fargaban kada maza su janye hannu wajen daukar nauyin iyalansu idan suka ga mata sun sami karfin kulawa da kansu.
Saurari cikakkar tattaunawar
Your browser doesn’t support HTML5