Wannan sanarwa ta janyo cece-kuce a cikin kasar, musamman ganin yadda zaben shugaban kasar yake kara karatowa, wanda za’a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa.
A hirar shi da Muryar Amurka, mai sharhi kan hakokin siyasa a Najeriya kuma Malami a Jami’ar Abuja, Dr. Faruk Bibi Faruk, ya ce a dai tarbiya irin ta siyasa ana sa ran cewa a dimokaradiyya duk lokacin da ka taba samun mulki, jama’a suka baka dama ka ci zabe, to kai kuma idan ka sauka sai ka rike girman ka, ba zaka sake fitowa ka cewa jama’a ga wani abin da kake bukata daga gare su kuma su sake yi maka a kan wani dan takara ba.
Ya ce amma wannan ba tarbiya ba ce irin ta shugabanni kamar su Obasanjo, wanda suna dawo su yi dumu-dumu a cikin harkar siyasa su rinka yin zabe irin na san ran su, suna son su kuma su ingizawa mutane wannan abun saboda idan an kafa gwamnati su shiga su rinka juya shugaban kasa, suna gani kamar su kadai suka yankewa Najeriya cibiya, sune suke gani cewa dole sai sun fada aji a Najeriya har karshen rayuwarsu.
Ya kara da cewa Obasanjo ba mutum ba ne da ‘yan Najeriya suka zabe shi saboda farin jininsa, illa saboda wadanda suka kawo shi kuma suka sa dole sai an bashi kuri’a ya ci zabe da suke zama yaransa na soja a da, irin su Babangida da Abdulsalami da dai sauransu. To shi a kansa bai taba yin tasiri da ya kawo akwatin zabe kofar gidansa ba kuma tabbacin cewa watakila ko a cikin gidansa ba zai iya cin zabe ba, kuma maganganun da yake yi suna tasiri ne kawai saboda kaico bayansa ba ta yi dadin kafin shi da kuma bayansa ba.
Dangantaka Tsakanin Obasanjo Da Atiku
Da yake amsa tambaya dangane da yadda Obasanjo ya yi watsi da tsohon mataimakinsa Alhaji Atiku Abubakar da yake yiwa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a yanzu, Dr. Faruk, ya ce dama can akwai tsamin dangataka tsakanin Obasanjo da Atiku, an danne Obasanjo ne tuntuni a lokaci da Atiku ya yi wadancan takarkarin, aka rinka sa shi ya goya masa baya dole saboda wadannan yaransa wanda da ma su ne tasirin rayuwarsa ta siyasa da samun mulki da ya yi tayi, su Babangida sun karba sun ce a’a a yi Atiku a lokacin shi kuma yana ganin baya son ya ja da su.
Ya ce to a yanzu a wannan kungiyar tasu da suke ganin sune iyayen Najeriya, wanda su Babangida da T. Y. Danjumma da ragowar tsoffin sojojin Najeriya, Obasanjo yana ganin a karshen rayuwarsa a shekarunsa da suka kai kusan 90, yana son ya mutu ana cewa ya kaunacin kudancin Najeriya.
Yawan Jama’a Da Bangaranci
Da yake tsokacin kan yawan jama’a da bangaranci, Dr. Bibi Faruk ya ce ita siyasa tana da wani abu wani kuskure da ‘yan Najeriya suka dauka suna yi, duk ran da ka dauki yawan jama’a ka hada shi da bangare, to bangare da yawan mutane idan ya hadu aka ce a kan sa za’a tabbatar da magana ta siyasa to rigima ce take ballewa, saboda wasu za su ga sun cancanta saboda kawai bangare da suke ciki a’a su a gabas suke ko kudu ko arewa.
Ya ce wasu kuma zaka ga sun cancanta kawai saboda su suka fi yawa, to yawanci sai bangaranci ya kawo cancantarsa ta karfi, idan aka hadu gwabzawa ake yi, duk inda aka yi wannan hadin rigima ake yi, to amma ‘yan Najeriya a hankali a hankali, musamman 'yan kudancin Najeirya sun dauki wannan magana sun maida ita dole sai a yita ta bangaranci.
Rabuwar Kan ‘Yan Najeriya
Da yake tsokacin kan maganar rabuwar kan ‘yan Najeriya, Dr. Bibi Faruk ya ce akan cewa ana da maganar dole cewa sai an yi kudanci ko arewaci, akwai yadda da ake da ita a tsakaninsu kamar yadda ita Najeriya ta ce idan aka dauko abu aka raba duk wanda suka samu kan su a cikin wannan rabuwa za su yi daga da wadanda ba sa cikin wannan rabuwa, amma kuma da an dauke kafa an kyale su a cikin na su bangaren sai wata rabuwar ta sake zuwa wacce tafi tasiri akan wacce da take nan.
Ya ce yanzu a kudun idan aka zo aka bar Obasanjon da ana kudun da arewacin kuma wanda su shugaban arewacin suka dauke kai suka bar shugabannin ‘yan kudun, to kuma rigimar da take cikin kudun tsakanin Yarabawa da Inyamurai wata sabuwar rigima ce.
Shawara Kan Kalaman Manyan Najeriya
Dangane da shawara kuma, Dr. Bibi Faruk ya ce, manyan Najeriya basa nuna alkunya na jama’arsu ko kuma kauna ta tunani me makomar kasarsu za ta zama, maimakon a rinka irin abubuwan da zai hada kan jama’a, yasa kasa ta samu albarkar yawanta, wato karfin da take da shi na tattalin arziki ya bunkasa sai a rinka maganar rabe-rabe ko da an girma an zama dattijo.
Saurari hirar Dr. Bibi Faruk Da Mohammed Hafiz Baballe:
Your browser doesn’t support HTML5