Kamfanin Google, zai samarwa mutane hanya mafi sauki da zasu rinka samun bayanai lokacin da wata masifa ta taso, ta hanyar SOS alert dake cikin taswira da kuma runbun binciken Google.
An tsara hanyar fadakarwar ne domin tunkarar duk wata masifa da ta taso kamar girgizar ‘kasa ko guguwa ko kuma harin ta’addanci.
Duk mutanen dake kusa da inda wata annoba ta taso kuma suke neman bayani ta kafar Google, zasu samu cikakken bayanin da ya hada da inda zasu sami taimakon gaggawa, su kuma san halin da ake ciki a yankin da suke.
An kirkiri SOS alerts da hadin gwiwar kungiyoyin agaji daga kasashe 12, amma wannan fasaha zata kasance a kowacce kasa a fadin duniya.
Ma’aikatan kamfanin Google zasu rika zakulo bayanai daga gwamnatoci da sahihan kafafen yada labarai domin samarwa da mutane bayanan da suke bukata.
Google dai ya kwashe watanni yana ta gwajin wannan fasaha. Ya kuma ce yayi amfani da ita wajen aikawa da sakon gaggawa lokacin da gobara ta barke a dogon ginin nan da ake kira Grenfell Tower, wanda mutane dayawa dake yankin suka samu.
Fasahar SOS alerts za tayi aiki da fasahar neman mutanen da suka bata ta, wadda ke nemo bayanai kan mutanen da suka bace a lokacin faruwar wata masifa.
Google ba shi bane kamfanin farko da ya fara samar da wannan fasaha ba, Facebook ma yana da nashi irin fasahar wadda mutane ke iya sanar da cewa suna lafiya a lokacin faruwar wata annoba ko masifa.
Your browser doesn’t support HTML5