Google Na Bada Damar Satar Bayanan Sirri Na Mutane

Kamfanin Google ya ansa cewar wasu sakonnin sirri da akan aika ma mutane ko su aika, (Email) wasu na karanta sakonnin, matsalar ta samo asali ne daga masu kirkirar manhaja da na’urori.

Mutane da suka saukar da tsarin manhaja da wasu kamfanoni suka kirkira wajen duba asusu su na google, zasu iya shiga cikin jerin wadanda zasu iya fuskantar wannan matsalar ta satar bayanai.

Wani kamfani ya bayyana ma kamfanin dillancin labarai na “Wall Street Journal” cewar wannan al’adar ba bakuwa bace ta karanta sakonnin mutane daga wasu mutane. Domin kuwa kamfanin na google ya ayyana cewar hakan bai sabama ka’idojin kamfanin ba.

A tabakin wani mai sharhi kan tsaro, wanda ya bayyana cewar hakan abun mamaki ne aga shahararren kamfani kamar Google yana bada damar satar bayanan jama’a.

Gmail shine shafi mafi girma a duniya idan aka yi maganar aika sakonnin yanar gizo, wanda yake da mutane sama da billiyan 1.4 a fadin duniya suna amfani da shafin wajen aikawa da karbar sakonni.

Kamfanin na Google yakan bar mutane su hada asusun su da wasu manhajoji wanda hakan kan kai mutun shiga cikin jerin mutane da za’a iya karanta labarin su.