Gobe Shugaba Buhari Zai Sa Hannu A Kasafin Kudin Shekarar 2020

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmed Ibrahim Lawan, ya fada wa Muryar Amurka cewa ya na da tabbacin cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai sa hannu a Kasafin kudin shekarar 2020 gobe Talata, 17 ga watan nan na Disamba.

Shugaba Mohammadu Buhari Zai Sa Hannu A Kasafin Kudin Shekarar 2020

Majalisar dokokin kasar ta yi kari akan kasafin da Shugaba Buhari ya tura mata daga Naira Triliyan goma da digo uku (10,330,416,607,347) zuwa Triliyan goma da digo biyar (10,594,362,364,830).

Shugaba Mohammadu Buhari Zai Sa Hannu A Kasafin Kudin Shekarar 2020

Majalisun duka biyu, sun amince da Kasafin tare da fatan za a fara aiwatar da shi daga watan Janairun shekarar 2020 zuwa Disamban shekarar sabanin yadda ake yi a baya.

Shugaba Mohammadu Buhari Zai Sa Hannu A Kasafin Kudin Shekarar 2020

Sanata Ahmed Lawan, ya ce Majalisar ba 'yar amshin Shata ba ce, jituwar da ke tsakaninta da bangaren gwamnati na nuni da cewa Majalisar ta na bin umurnin mazabu ne tare da yi wa al’ummar Najeriya aiki. Kuma duk abin da suka yi, babu wanda ya saba wa doka.

Ga rahoto ckin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Gobe Shugaba Buhari Zai Sa Hannu A Kasafin Kudin Shekarar 2020