Masu aikin ceto na kokarin zakulo gawawwakin yaran da suka babbake daga cikin karekitan motar safar 'yan makaranta a kasar Thailand wacce ta kama da wuta bayan da tayi hatsarin, da ake fargabar ya hallaka fiye da mutane 20.
Mummunar gobarar ta babbake motar dake kan wata babbar hanya a yankin arewacin birnin Bangkok yayin da take dauke da yara 38-da suka hada da kanana da matasa da malamai 6 dake balaguron 'yan makaranta.
Gawawwakin sun yi mummunar konewar da tasa hukumomi suka kasa tantance adadin wadanda suka mutu, sannan aikin tantance bayanan gawawwakin zai iya daukar kwanaki.
A cewar Ministan Harkokin Cikin Gidan Thailand, Anutin Charnvirakul mutane 21 sun tsira daga gobarar sai dai har yanzu ba a san inda 23 suka shiga ba amma ana kyautata zaton sun mutu.
Masu aikin ceton sun sanya shinge a kewayen tarkacen motar domin kange jami'an kashe gobara da masu bincike a yayin da suka fara aikin zakulo gawawwakin.