Gobarar dajin da ke ci a sassan Amurka da ke arewa maso yammacin gabar tekun Pacific, ciki harda arewacin jihar California, da Oregon, da Washington, ta lakume dubban gidaje, da masana’antu da kuma garuruwa.
Akalla fiye da eka miliyan na filaye gobarar ta lalata. Haka kuma Gobarar ta kashe akalla mutane 35 a fadin yankin.
Hayaki da kaurin wutar sun hade sun lulluɓe biranen San Francisco, da Seattle, da kuma Portland inda suka haifar da mummunan yanayin iska da ba a taba gani ba a duniya.
Hayakin da ya lulluɓe yankin na barazana ga lafiyar miliyoyin mazauna yakin.
Jami'an muhalli na jihar Oregon da ke arewa maso yammacin kasar sun bayyana yanayin iskar yankin a matsayin "mummuna” ko kuma mai tattare da haɗari ga bil’adama."