Gobara Ta Mamaye Dajin Los Angeles National Forest

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomi sun yi amfani da jiragen sama masu saukar ungulu da kuma helikofta don kashe gobara a dajin Los Angeles wato Los Angeles National Forest da ke Kudancin California, Alhamis, 30 ga Yuli. Mahukunta sun ba da umarnin masu matsuguni su bar gidajensu saboda gobarar, amma ba a sami jikkata ba.