Gobara Ta Lakume Kasuwar Robobi a Jihar Anambra

Wata gobara da ta lakume daruruwan shaguna a Kasuwar Danjabalu a Jihar Sokoto a 2020

Wata gobara da ta tashi da tsakar dare a birnin Onitsha da ke jihar Anambra a kudu maso gabashin Najeriya, ta haifar da asarar dukiyoyi.

Rahotanni sun ce ibtila’in ya faru ne da misalin karfe dayan daren Juma’a, amma babu wanda ya rasa ransa saboda babu kowa a kasuwar.

Bayanai sun yi nuni da cewa ba a san abin da ya haddasa gobarar ba, amma kafafen yada labaran Najeriya sun ce hukumomi suna binciken kan musabbabin tashin gobarar.

Hakazalika ana kan bincike kan iya adadin asarar dukiyoyin da aka tafka.

Wadanda suka shaida aukuwar lamarin sun ce mutane sun yi amfani da ruwan bokatai kafin zuwan jami’an kashe gobara, wadanda suka shawo kanta daga baya.

Kasuwar robobin ta Plaza, ta kasance babbar kasuwar da ta fi kowacce hadahadar kayayyakin roba irinsu bokatai, randuna da dai sauransu.

Onitsha, babban birnin jihar ta Anambra, ya kasance cibiyar kasuwanci da ke jan hankulan ‘yan kasuwa daga sassan Najeriya har da na kasashen waje musamman daga yammacin Afirka.

Gobarar kasuwanni a biranen Najeriya, ba bakon abu ba ne, ta kan faru musamman a lokutan huturu da ake ciki a yanzu, abin da kan kai ga asarar dubban miliyoyin kudade a wasu lokuta ma har da rayuka.