Gidauniyar ta Al-Mustapha tare da hadin gwiwar gidauniyar Samuel Fukat sun yaye dalibai fiye da dubu uku da aka koyawa sana'o'i iri-iri domin inganta rayuwarsu da samun dogaro da kai.
Daliban da aka yaye a gidauniyar S. P.Fukat dake garin Mangu cikin jihar Filato sun hada da mata da maza da yara da marayu har da magidanta.
An koya masu sana'o'i kamar yin sabulu, man shafawa, hada abincin kaji, tukin mota da dai sauransu.
Wasu daliban sun shaidawa Muryar Amurka abubuwan da aka koya masu da tasirin da horaswar zata yi a rayuwarsu. Wata Saratu Usman tace an koya masu sana'o'in cigaba sosai. Sun koyi yin sabulu, yogot, man shafawa da makamantansu. Kafin horon da suka samu suna zaune babu abun yi. Amma yanzu wasunsu sun soma yin aikin kansu suna cigaba.
Monday Bulus wani makaho yace an koya masa yadda zai yi sabulu. Ya iya amma sabili da nakasar da yake da ita ya hada hannu da matarsa domin su samu kudin cimaka da na biyan kudin makarantun yaransu.
Shugaban gidauniyar Fukat, Samuel Fukat yace ganin matsalolin da suka addabi arewacin Najeriya da suka haddasa karuwar marayu da rashin aikin yi tsakanin matasa yasa ya dukufa akan horas dasu. Makarantar ta marayu ce. Da yana biya masu kudin makaranta daga mutum daya har sun kusa dari. Yaran suna karuwa. Tun daga Borno sun samu karin yara marayu. Yanzu sun koyas da yara dubu uku da dari daya.
Yayin da yake kaddamar da cibiyar a garin Mangu Manjo Hamza Al-Mustapha yace lokaci yayi da gwamnati da masu hannu da shuni zasu taimaka wurin inganta al-ummar dake kewaye dasu. Idan wadanda Allah ya wadatar basu kula da talakawan dake kewaye dasu ba akwai hatsari. Abun da ya addabi arewa maso gabas daga rashin kula da talakawa ya samo asali. Yakamata a gyara wannan lamarin yadda kowa zai san shi ma da ne.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5