Gidauniyar Bill Gates Zata Samar da Maganin Kanjamau Mai Araha

Bill Gates da matarsa Melinda da suka kafa gidauniyar tare

Gidauniyar Bill Gates zata samar ma masu cutar kanjamau magani mai rahusa tare da basu taimako

Za a samarwa masu jinyar cutar kanjamau maganin cutar mai araha tare da tallafin kudi daga gidauniyar Bill Gates.

Cibiyar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ce ta sanar jiya alhamis cewa gidauniyar Bill Gate ta bada tabbacin daukar nauyin sarrafa wani adadin maganin, yayinda kamfanonin sarrafa magungunan kuma suka amince su kayyade kudin maganin zuwa dala saba’in da biyar kan kowanne majinyaci a shekara.