Gidauniyar Aisha Buhari Za Ta Gina Dakunan Kula Da Mata Da Kananan Yara a Asibotoci

Matar Shugaban Kasa Aisha Buhari Ta Kaddamar Da Ofishin Ayyuka Ga Mata Masu Kananan Sana'a

A wani sabon yunkuri na magance matsalar mace-macen mata da kananan yara a Najeriya, gidauniyar matar shugaban ‘kasa Aisha Buhari ta kaddamar da shirin gina wasu dakunan kula da mata da kananan yara a manyan Asibitocin Najeriya, wanda tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.

Wannan shiri na gidauniyar da uwar gidan shugaban ‘kasa Aisha Buhari ta kafa mai taken Future Assured, dake da zimmar rage mace-macen mata ya yin haihuwa da kuma kananan yara.

Kamar yadda alkalumma suka nuna a Najeriya, mata da dama ne a kullum ke mutuwa baya ga kananan yara sakamakon rashin zuwa Asibiti ko cibiyoyin kiwon lafiya, lamarin dake ‘kara barazana a yanzu.

Domin tallafawa wajen ragen wannan matsalar ne yasa cibiyar Aisha Buhari ta gina dakunan kula da mata da kananan yara a babban Asibitin daura, dake zama mahaifar shugaban kasa, haka kuma yanzu ta kawo irin wannan gudunmawar a babban Asibitin tarayya FMC, dake Yola, yayin da take haramar fadada shirin zuwa wasu yankunan kasar.

Dr Muhammad Kamal, dake zama likitan matar shugaban kasan shi ya jagoranci tawagar gani da ido na yadda aikin ke tafiya a Yola.

Shima da yake tsokaci, shugaban asibitin FMC, Farfesa Awwal Muhammad ya bukaci kungiyoyi da kuma masu ruwa da tsaki, da suma suke bada nasu gudunmawar wajen bunkasa harkar kiwon lafiya a Najeriya.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Gidauniyar Aisha Buhari Za Ta Gina Dakunan Kula Da Mata Da Kananan Yara a Asibotoci - 3'31"