Ranar Ashura, 10 ga watan Muharram, rana ce mai muhimmanci ga duk Musulman duniya. Wasu bangaren Musulmai su na gudanar da azumi a wannan rana domin kwatanci da Annabi (SAW). Amma ga ‘yan Shi’a, rana ce ta jimami domin kisar da aka yi wa Imam Hussaini, jikan Annabi (SAW), a Karbala a shekarar 680 Miladiya.
Daruruwan ‘yan Shi’ar Ghana, maza da mata, sanye da bakaken kaya sun yi tattaki a wasu titunan birnin Accra suna bugun kirji suna raira wakoki domin bayyana bakin cikin kisar Imam Hussaini, jikan Manzon Allah (SAW) da aka yi a Karbala dake kasar Iraqi.
Mabiyan sun hadu a hedikwatarsu dake unguwar Mamobi, Accra, suka yi jerin gwano cikin tsari da jagorancin ‘yan sanda, suka bi ta babban titin Nima zuwa unguwar Newtown, sannan suka karasa zuwa filin wasan zamani na Wembley dake unguwar Kotobabi, inda sauran mabiya daga unguwanni daban-daban suka jero aka hadu a wannan filin wasa.
AbdulAziz Haruna Futa, daya daga cikin wadanda suka tsara tattakin ya nuna cewa suna bin tsari ne kamar yadda dokar kasa ta ajiye. Sai da suka nemi izinin ‘yan sanda sannan suka gudanar da tattakin, kuma sun yi tanadin motar daukar marasa lafiya domin taimakon gaggawa idan bukatar hakan ta taso.
A jawabinsa ga mabiya, babban limamin Shi’a na Ghana, Sheikh Abubakar Kamaludden, ya yi kira gare su da su yi hakuri da juna, kada su dinga kullatar juna a zuciyarsu.
Gabanin nan, Shugaban Majma Ahlul Bait na Ghana, Sheikh Muhammad Abu-Jajah ya gaya wa Muryar Amurka cewa wasu da suke tattsaga bangarorin jikinsu har jini na zuba, gurbatattu ne a cikin Shi’a. Ainihin ‘yan Shi’a na kwarai ba su aikata hakan.
Wasu mabiya Shi’a sun bayyana bakin cikinsu a kan abinda ya faru da Imam Hussaini da mabiyansa a Karbala; inda suka ce lallai suna jimamin kisar da aka yi masa.
An gudanar da irin wannan tattakin a sauran yankunan kasar Ghana.
Saurari cikakken rahoton daga Idris Abdullahi:
Your browser doesn’t support HTML5