Wani jirgin sama dauke da allurai 600,000 na rigakafin AstraZeneca-Oxford na Jami’ar Oxford ya isa Accra babban birnin kasar a ranar Larba, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa daga WHO da UNICEF, Asusun Bayar da Agajin Gaggawa na Yara na Majalisar Dinkin Duniya.
Cibiyar ta Serum ta Indiya, wace ita ce masana’antar rigakafi mafi girma a duniya, ita ce ta kirkiro allurar rigakafin.
An sayo alluran rigakafin da aka aika zuwa Ghana ta hanyar COVID-19 Vaccines Global Access Facility, ko COVAX, wanda wani shiri ne da hukumar WHO ta kaddamar tare da hadin gwiwar Hadakar Masu Yaki Da Annoba ta Coalition for Epidemic Preparedness Innovation, Gavi, da Gamayyar Masu Samar Da Rigakafi ta The Vaccine Alliance, da kungiyar da masu hannu da shuni ta Bill da Melinda Gates suka kafa don yiwa yara rigakafi a kasashe mafi talauci na duniya.