Ghana Na Kokarin Yin Akasarin Magungunata a Cikin Gida

BRITAIN-UN-CLIMATE-COP26-ghana

A wata hobbasa ta kokarin wadata ingantattun magunguna a Ghana, masana a harkar hada magunguna, sun yi kira ga hukumomin kasar Ghana da su kara azama wajen ganin an samar da hanyoyin sarrafa wasu magunguna a cikin gida, domin kauce wa matsalar dogaro da kasashen wajen.

Atlantic LifeScince Ltd, Babban kanfani ne da ke shigowa yana rabon magugunan yaki da macizai da haukar kare a nahiyar Afurka ta yamma. Bayan bayyanar cutar Covid 19, kamfanin ya kara sarafa wasu muhimman magunguna da za su taimaka wajen yaki da covid 19 ta tsarin dogara ga kai na gwamnati. Babban Jami’in zartaswa wanda kuma shi ya assasa kamfanin, Dr Dhananjay Tripathii, ya yi kira ga gwamnati da ta rage sayo maguguna da za a iya sarafa su a gida, daga kasashen ketare.

Ministan Masana’antu da, treda Alan kyeremanteng, ya bayyana cewa hanya mafi sauki na janye kasar daga dogara akan sayo maguguna daga ketare shi ne karfafa masana’antar sarrafa magani na gida .

Shugaba Akufo Addo ya ce samar da aikin yi kai tsaye guda 380 da kuma ayyuka wadanda ba na kai tsaye ba 2500 zai rage matsalar rashin aikin yi a kasar Ghana.

Shirin gunduma daya, masana'anta daya na mai da hankali kan samarwa da kuma inganta harkokin kasuwanci masu inganci don tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ga al'ummomin karkara. Bugu da kari, shirin 1D1F ya yi kokarin magance kalubalen talauci da ke yaduwa da kuma kara cigaba a tsakanin al'ummomin karkara. Atlantic Lifesciences Ltd ya dau mataki a cikin 2017 tare da goyon bayan gwamnati don kafa wannan sabon wurin a fannin kiwon lafiya , tare da tsunduma a cikin masana'antun magugunan rigakafin cizon maciji , maganin diga wa ido , maganin kashe zafi ko ciwo, allurai da kwayoyin magani ko capsules a Lakpleku karkashin shirin gunduma 1 masanaanta daya.

Saurari rahoton Ridwan Muktar Abbas:

Your browser doesn’t support HTML5

Magunguna a Ghana