Rikicin baya bayannan ya samo asali ne biyo bayan halbe wasu matasa su uku har lahira yayinda suke kan hanyarsu zuwa gida daga garin Bolgatanga a jahar maso gabashin kasar Ghana.
A hirar shi da Muryar Amurka, Mallam Usman Adamu mai inkaya da Apuuman, wani mutum da ya tsallake rijiya da baya ya bayyana yadda lamarin ya faru.
" mun isa Bolga ne domin gudanar da wasu harkokinmu, bayan mun kammala muka kama hanya zuwa Bawku ne wasu matasa dauke da adduna suka tsare mu daf da wata makarantar sakandari kana suka bude mana wuta..Sun halbe mutum uku daga cikin mu amma ni tare da direban motar ne muka tsira da ranmu.Muna cikin fargaba sosai .
Shi kuwa Mallam Irbad Ibrahim mai sharhi bisa harkar tsaron ciki da wajen Ghana ya bayyana cewa gwamnati na zuba zuzurutun kudade domin tabbatar da zaman lafiya a yankin amma yunkurin ya ci tura. Ya kuma bukaci da masu ruwa da tsaki su bada gudunmuwa wajen samarda zaman lafiya.
"kudadenda ake kashewa wajen tsaro a Bawku ' da za baiwa wasu hannun jari ne da ya taimaka ma garin Bawku adon haka muna rokan dattawa da sarakuna da limamai da matasa da su bar asamarda zaman lafiya aBawku", inji shi.
Shaikh Salam Hassan mamba a majalisan wanzar da zaman lafiya a Ghana ya bayyana cewa sun gana da bangarori biyun kuma su duk suna neman zaman lafiya amma kuwa akwai wadanda ke gefe suna hura wutar rikici. Ya kara da cewa gwamnatin Nana Addo na kokari domin samar da zaman lafiya ayankin. Yace, "Gwamnati ta yi nata kokari saboda kowane lokaci akwai jami'an tsaro awajen domin a kiyaye rayuka da amanar mutane."
Wani saurayi da ya bayyana sunansa a matsayin Hafiz mazauni Zangon Bawku da ya tsere domin neman mafaka yace tashin hankali ya yi sanadiyar sauya matsuguninsu zuwa kudancin kasar Ghana.
Hukumar 'yan sanda ta ce bata cafke kowa ba tukuna amma an samu kwanciyar hankali a yankin kuma tana ci gaba da gudanar da bincike, yayinda ta ke kokarin maido da doka da oda.
Rikicin kabilanci na daga cikin matsalolin da ke maida hannu agogo baya a kokarin da gwamnati ke yi wajen samar da cigaba musamman a yankin jahar maso gabashin kasar abinda yayi sanadiyar ficewar jama'a da dama ayankin.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adam cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5