Ghana: Majalisar Sarakunan Gargajiyan Zango Ta Yi Kira A Gudanar Da Zabe Cikin Lumana

Taron Sarakunan Gargajiya a Ghana

A baya-bayan nan, an samu rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyar NPP mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta NDC, a unguwar Maamobi dake birnin Accra da kuma garin Ejura dake yankin Ashanti, wanda ya kawo damuwa ga shugabancin al’ummar Zango.

Majalisar sarakunan gargajiya ta Zangunan yankin Greater Accra, ta shiga jerin kungiyoyin addinai da na farar hula, da suka yi kira ga mabiya jam’iyyun siyasa, musamman matasa, da su tabbatar da tsarin dimokradiyya ta hanyar fifita zaman lafiya gabanin zabe, lokacin zabe da kuma bayan zaben 7 ga watan Disambar 2024 dake kara karatowa.

Kusan dukkanin zabukan Ghana da suka gabata, galibin wuraren da ake yawan rikici, inda jami’o'in tsaro suka yi wa lakabin ‘hotspot’, suna cikin unguwannin Zango dake fadin kasar Ghana ne.

Taron Sarakunan Gargajiya a Ghana

A baya-bayan nan, an samu rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyar NPP mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta NDC, a unguwar Maamobi dake birnin Accra da kuma garin Ejura dake yankin Ashanti, wanda ya kawo damuwa ga shugabancin al’ummar Zango.

Bayan an kammala taron, mukaddashin shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Zangunan Accra, Sarki Abubakar Siddick Jimala da ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su koma gida su yi wa al’ummarsu bayanin muhimmancin tabbatar da zaman lafiya a zabe mai zuwa.

Taron Sarakunan Gargajiya a Ghana

Ya ce ‘'Sarakai, idan fitina ta zo, ba mu da wurin zama, domin haka mu yi wa kowa nasiha cewa siyasa abu ne na hadin kai da ci gaba. Mu yi kokari mu educate (ilmantar) da yaran mu’'.

Sheikh Armiyau Shu’aibu, mai magana da yawun limamin limamai na kasa, Dokta Usman Nuhun Sharubutu, ya yi kira ne da ‘yan Zango su daina yarda ana jan matasansu zuwa ga tarzoman siyasa.

Taron Sarakunan Gargajiya a Ghana

Ya kara da cewa, duk sarakuna su yi amfani da sarakunan samari da suke karkashinsu wurin wayar da kan matasansu, kuma kafin 7 ga watan Disamba da za a gudanar da zabe, a duk wani ‘taro da za mu yi, a samu wani daya daga cikin manyan sarakunanmu ya tashi ya ba da sakon a yi hattara’.

Sheikh Shuaibu yace, burin limamin limamai na kasa, mai shekaru 105, ne idan lokacinsa ya kai, ya bar Ghana cikin lumana.

Taron Sarakunan Gargajiya a Ghana

Wanda ya wakilci, tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama, dan takaran shugaban kasa na jam’iyar NDC, Alhaji Mustapha Abubakar Masloc yace: ‘John Dramani Mahama ya ba da busharar cewa, shi ba zai yarda a zubar da jini domin a dauke shi sarauta (a zabe shi) ba’.

Haka kuma wakilin mataimakin shugaban kasa Alhaji Mahamudu Bawumia, dan takaran shugaban kasa na jam’iyar NPP, Dokta Yunusa Osman Mohammed, a gefen taron ya isar da sakon mataimakin shugaban kasa.

Ya ce "Dokta Bawumia na kira ga duk ‘yan Ghana da su kiyaye daga tashin hankali. Muna kira ga kowa, manya da yara da su kwantar da hankalinsu, a yi shiri a je lokacin zabe a kada kuri’a, kuma kada ya yarda a yi amfani da shi ko ita wurin tayar da tarzoma'’.

A hedkwatar ‘yan sandan Ghana dake Accra kuwa, hukumar tsaro ta musamman da ke kula da harkokin zabe ta kasa (NESTF), a karkashin jagorancin sufeto-janar din ‘yan sanda (IGP) Dokta George Akuffo Dampare, ta gudanar da tattaunawa da shugabannin jam’iyyun siyasa kan shirye-shiryen tsaro a zabe mai zuwa.

Taron Sarakunan Gargajiya a Ghana

Sufeton ‘yan sandan ya kara jaddadawa shugabannin jam’iyyun sadaukarwar da hukumar ke yi na samar da ingantaccen yanayin zaɓe.

Ya ce, '‘babu son kai a ayyukan da za mu gudanar kuma doka ce za ta zame mana jagora, kuma duk wanda ya karya wadannan dokokin, lallai zai fuskanci doka,” in ji IGP.

Saura kwanaki 15 a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki a Ghana.