Jiya daya ga watan Mayu ce ranar kwadago ta duniya a dalilin haka ne ma’aikatan kasar Ghana suka yi dafifi a filin kwallon wasa na Baba Yara dake Kumasi.
Babban magatakardan kungiyar kwadagon kasar Dr Anthony Yaw Baah shi ya shugabanci shirya bikin na wannan shekarar. Bikin ya hada da wake wake da raye raye da maci tare da nuna tutocin kungiyoyin dake hadakar kungiyar ma’aikatan. Ma’aikatan suna dauke da kwalaye masu rubuce rubucen sakonninsu zuwa gwamnati. Misali suna kira a kara masu albashi tare da basu aikin yin a kwarai.
A cikin jawabin da ya yi babban magatakardan ‘yan kwadagon ya tabo batun dangantaka dake tsakaninsu da ma’aikatan kasar Cuba da fatan za’a karfafata. Ya kuma yi tsokaci akan abun da ya kira karancin aiki mai kyau a Ghana.
A cewar Dr. Baah daga cikin ‘yan Ghana miliyan 14 da suka cancanta a basu aiki miliyan biyu kacal suke da aiki mai kyau yayinda sauran na nan kara zube. Bugu da kari wasu miliyan goma sha daya suna aiki ne a wani mummunan hali da bashi da wata kyakyawar fata gobe.
Shugaba Akufo Adoo ya jinjinawa ma’aikatan kasar saboda yadda suke tuntubar juna domin samun masalaha daga matsalar da suke ciki. Ya basu tabbacin abun da gwamnatinsa zata yi domin samar da ayyukan yi tare da taimakawa matasa. Zasu yi kokari su warware matsalar yin anfani da yara a aikin kwadago kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tanada. Ya ce abun takaici ne yadda wasu suka yi kunne uwar shegu akan saka yara cikin kwadago. Sun birije da kiran su daina anfani da yara ba tare da basu ilimi ba.
Wasu ma’aikatan da aka zanta dasu sun yaba da bikin. Sun ji dadin kasancewar shugaban kasar a bikin tare da kalamun da ya yi.
Ridwan Abbas nada karin bayani a wannan rahoton
Your browser doesn’t support HTML5