Gawmnatin Najeriya Ta Koka Kan Rahoton Amnesty International

Muhammadu Buhari

Ministan Labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya koka bisa yadda rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar dake zargi sojojin Najeriya da laifin danne hakkin bil'adama a kasar.

Lai ya ce yayin da ake kashe sojoji sai kowa yayi shiru, amma yayin da sojojin ke kwantar da tarzoma sai ai masu cha, tamkar kashe sojojin daidaine, sannan ya kara da cewa wadannan sojoji suma za su so su zauna a barikokinsu, amma saboda tsare baki dayan al'umma su ke filin daga.

Amma kakakin Amnesty International a Najeriya Isa Sanusi, ya ce ba zasu sa ido haka kurum ana cin zarafin dan adam ba, don shi kansa yakin da sojojin ke yi ai don Jama'ar ake yi.

Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta kuma ce kimanin mutane dubu biyu da dari shida suka rasa rayukansu a rigingimun makiyaya da manoma. A cewar shugaban makiyaya na Kulen Allah ta kasa Khalil Mohammed Bello, ya ce abubuwa da dama sun shigo cikin al'amarin, don haka adadin ka iya wuce haka.

Ga Hassan Maina Kaina da cikkaken rahoto