Gasar AFCON: Najeriya Za Ta Kara Da Kamaru A Zagaye na Biyu

Tawagar Najeriya a gasar cin Kofin Nahiyar Afirka za ta kara da Kamaru a zagaye na biyu a gasar da a ke fafatawa a kasar Kwaddebuwa.

Za a buga wasar a ranar 27 ga watan Janairun da mu ke ciki karfe bakwai agogon GMT a filin wasa na Felix Houphouet- Boigny da ke birnin Abidjan.

Najeriya ta samu hayewa bayan ta yi kunen doki a wasanta na farko da kasar Equitorial Guinea kafin ta ci Kwaddebuwa, masu karban bakuncin gasar da Guinea Bissau ci 1-0 kowannensu.