Garzali Miko Na Shirin Angwancewa

Garzali Miko (Instagram/Garzali Miko)

Mawaki kuma jarumin Kannywood Garzali Mika’ilu, wanda aka fi sani da Garzali Miko ko Gaza, na shirin shiga daga ciki.

Katin gayyatar da jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram ya nuna cewa a ranar Juma’a 20 ga watan Agusta za a daura auren da amaryarsa mai suna Habiba Umar Dikwa.

“Iyalan Alhaji Mika’ilu Mai Lema da na Marigayi Alhaji Umar Ahmad Dikwa na gayyatar ku wajen daurin auren Garzali Mika’ilu Mai Lema da Habiba Umar Dikwa.” Katin da jarumin na fim din ‘Hasashe’ ya wallafa a shafinsa na Instagram ya nuna.

Bayanai sun yi nuni da cewa a ranar Talata aka bude shagulgulan bikin wanda aka tsara zai kunsa har da wasannin kwallon kafa kamar yadda Mujallar Fim ta ruwaito.

Garzali Miko (Instagram/ Garzali Miko)

“Allah ya ba da ikon zuwa Ameen.” Garzali ya ce.

Tuni fitattun jarumai irinsu Ali Nuhu, wanda Garzali ya yi aiki a karkashinsa, shi ma ya wallafa katin gayyatar a shafinsa na Instagram.

Masoyan jarumin maza da mata su ma sun yi ta rige-rigen taya shi murnar auren nasa a shafukan sada zumunta.

“Allah ya sanya alkhairi ogha” In ji bsd_brother_dorayi.

“Allah ya ba da zaman lafiya.” In ji Idris_hawau.