A baya Notley da hukumomin garin sun yi ammanar cewa, wutar ta cinye ilahirin birnin, to sai gas hi a shawagin da aka yi ta sama a jiya Litinin ya nuna cewa wurare kadan ne wutar ta cinye ba yadda aka yi zato ba.
Ta bayyana cewa, “wuta da ta tashi gadan-gadan a garin a kwanakin da suka shude, sai gashi birnin Fort McMurray da alummarsa sun tsira, sannan za’a taimakawa mutanen garin”. Inji Notley.
Ta kuma godewa ma’aikatan kashe gobara game da kokarinsu da suka yi don cetar garin daga babbakewa, duk kuwa da rasa wutar lantarki da ruwan fanfo. Firimiyar tace zai kai mako daya nan gaba kafin al’ummar birnin su koma muhallansu.
Jami’ai a kasar suka ce, wutar dajin tana ta ci har a jiya Litinin, amma cikin ikon Allah sai aka sami canjin yanayin sanyi da kuma ruwan sama, wanda ya taimaka matuka wajen baiwa masu aikin kashe gobarar kwarin gwiwa.
Alberta dai nan ne gari na uku a duniya da suka fi ko ina ajiye rarar man fetur in ka dauke kasashen Saudiyya da Venezuela. Sannan wutar bata kai kan ko daya daga cikin harabar da gangunan man fetur din suke ba.