Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muguwar gobarar kasar Canada ta soma lafawa


Yadda hayakin wuta ya mamaye birnin Fort McMurray
Yadda hayakin wuta ya mamaye birnin Fort McMurray

A karon farko an soma samun labaru masu dadin ji dangane da muguwar gobarar nan da ta lakume yawancin yankin Alberta a yammacin kasar Canada

Firirmiyan Alberta Rachel Notley tace gobarar da ta tashi a yankin bata kai yadda mahukunta suka yi tsammani ba.

Norley tace ba kamar yadda masana harkokin gobara suka yi harsashe ba inda suka ce zuwa Lahadi gobarar zata ninka biyu, amma bata yi hakan ba maimakon hakan ma sai ta ragu. Kuma gobarar bata tsallaka zuwa jihar Saskatchewa ba kamar yadda aka yi zato, jiha dake makwaftaka da Alberta.

Jami'in kwana-kwana na jihar Alberta Chad Morrison yace ni'ima da aka samu ta taimaka wurin yaki da gobarar kuma ta ba 'yan kwanakwana su karkata gobarar ta yadda zata mutu.

Har zuwa jiya Lahadi gobarar ta lakume kadada 161,000 a arewacin Alberta kuma wutar na cigaba da ci. Dubun dubatan mutane ne yanzu suka nemi mafaka a wuraren agajin gaggawan da aka tanada.

Gobarar ta kusa lashe birnin Fort McMurray gaba daya inda ta tilastawa mutane 88,000 barin muhallansu ba tare da sun samu sun fitar da duk kayansu ba baicin rayukansu.

Brnin Fort McMurray yana cin wuta
Brnin Fort McMurray yana cin wuta

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG