Daruruwan jama'a ne suka dinga kwararowa daga Damboa zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno sakamakon harin da 'yanbindiga suka sake kaiwa garin tun daga daren shekaranjiya zuwa wayewar garin jiya.
Ganao sun shaidawa Muryar Amurka cewa maharan sun shigo garin da yawan gaske dauke da muggan makamai inda suka dinga cillawa gidajen mutane wuta da kuma harbin kan mai uwa da wabi.
A makonni biyu da suka gabata maharan sun afkawa jami'an tsaro dake cikin garin suka kashe jami'an 'yansanda da na soja. Tun a wancan lokacin ne jami'an tsaro suka fice daga garin kuma basu sake komawa garin ba. Tun a lokacin mutanen garin ke zaune ba tare da samun wani taimakon tsaro ba. Dalili ke nan maharan suna shiga garin suna cin karensu ba babbaka.
Alhaji Komi Damboa daya daga cikin dattawan garin Damboan da suka jagoranci 'yan Damboa zuwa fadan mai martaba Shehun Borno domin mika kokensu akan irin masifar da suka shiga. Alhaji Komi yace 'yanbindigan suna cikin riguna irin na sojoji. Saboda haka ba sani ba sabo suka kashe mutane goma sha shida. Sojoji kuma sun nuna bacin ransu sun ki komawa garin. 'Yansanda ma bayan an kashe DPO nasu su ma sun tara nasu ina su sun bar garin.
Alhaji Komi yace akwai bukatar gwamnati ta kawo masu doki ganin irin wahalar da suka shiga. Shehun Borno ya taimaka wajen kwantar da hankalin mutane. Lamarin da ake ciki yanzu sai dai gwamnati ta kawo tallafi domin jama'a basu iya sun yi noma ba. Abincin da suke dashi 'yanbindigan sun kona kurmus.
Wani Alhaji Sintiri yace an fara rikicin tun wajen karfe biyar na yamma har zuwa karfe biyu na dare. Idan ba gwamnati ta taimaka ba da tsaro garin shi ke nan ya fada hannun 'yanbindigan ko kuma ya watse gaba daya.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5