Gardama Kan Wurin Zama A Jirgin Kasa Ta Kai Ga Mummunan Cizo

Ranar juma'ar da ta gabata, wata kotu a birnin New York na kasar Amurka ta tuhumi wata mata da laifin kai farmaki, a sakamakon cizon da ta dankara ma wata fasinja sau da dama, a lokacin da suke rikici akan wurin zama a cikin jirgin kasa.

Matar ta dankarawa abokiyar tafiyar tata cizo ne a unguwar da ake kira Queens kusa da Manhattan a yayin da matar mai shekaru 45 ta shiga jirgin sannan ta umurci daya matar da ke zaune da ta matsar da kayan ta domin ta zauna.

Kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan gundumar yankin ya bayyana, matar dake zaune ta yi kunnen uwar shegu da ita, sai kawai ita kuma ta zauna kusa da matar da ke zaune da kayanta a gefe guda, sai kwatsam suka fara rigima.

Rahotanni sun bayyana cewar matar da ke zaune da kayanta ta mike tsaye ta cika hannu da sumar kan daya matar, sannan ta ci gaba da yakushinta da kumba daga karshe kuma ta gaggantsara mata cizo wanda saboda tsananin zafi matar, da tsayawar wannan jirgi sai matar ta afka da gudu ta fita.

'Yan sanda sun kama matar ne a yayin da suka yi anfani da hoton da wadda aka ciza ta dauki mai cizon da kuma hoton cizon akan kirjinta.