Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsarin Sabuwar Manhaja Ga Matasa 'Yan-Makaranta


Kamfanin Google
Kamfanin Google

Kamfanin google ya sanar da wasu sababbin canje-canje da yayi a tsarin su na sabuwar shekarar makaranta, a wanna karon. Wannan wani tsari ne wanda yake ba ma malamai da dalibai damar gudanar da darasi ta yanar gizo.

A wannan karon ma’aikatan kamfanin, sun yi tattaki cikin lungu da sako don fahimtar da al’uma wajan amfani da wannan tsarin nasu na ilmantar da jama’a. Domin kuwa sun samar da wata sabuwar manhaja, ta yanar gizo da mutane za su iya amfani da ita, wajen gabatar da darasi ga dalibai batare da sun biya komi ba.

Wannan wata dama ce da malamai kan tsara yadda dalibai za su gudanar da karatu, a gidajen su kuma su aiwatar da aikin gida don aika ma malami yagani a kowane lokaci. A duk cikin wannan tsarin akwai damar dalibai su gana da sauran ‘yan uwansu, dalibai dasu ke a fadin duniya domin ilmantar da juna da fadada fahimta.

Wannan sabon tsarin zai bama malamai damar gane fahimtar dalibai take, a kowane lokaci, domin kuwa malamai zasu dinga ganin yadda dalibai ke ganawa da sauran dalibai, wajen kawo fahimtar kowa a wani darasi ko muhawara da malami ya rubuta don kowa ya bada tashi gudunmawa a ajin.

Kana kuma wannan sabon salon zai taimaka ma malamai su da kan su, domin kuwa suna da damar haduwa a matsayin su na malamai a ko ina, don tattauna matsalolin dake addabarsu da kuma neman shawara ga abokan aiki, don samun hanyar magance matsalolin dalibai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG